logo

HAUSA

AU ta bayyana goyon bayanta ga Turkiye da Syria yayin da mummunar girgizar kasa ta auka musu

2023-02-07 10:50:17 CMG HAUSA

 

Shugaban hukumar kungiyar Tarayyar Afrika AU, Moussa Faki Mahamat, ya bayyana goyon tarayyar ga Turkiye da Syria, yayin da iftila’in girgizar kasa ya aukawa kasashen.

A sakon da ya wallafa a shafin tweeter, Moussa Faki Mahamat ya ce, nahiyar Afrika na nuna goyon baya tare da jajantawa gwamnatoci da al’ummomin Turkiye da Syria, biyo bayan mummunar girgizar kasa da ta yi sanadin mutuwar mutane sama da dubu tare da lalata gine-gine a kasashen. (Fa’iza Mustapha)