logo

HAUSA

Kasar Sin ta yi kira da a gaggauta kawo karshen rikicin Ukraine

2023-02-07 10:49:32 CMG HAUSA

 

Mataimakin zaunannen wakilin Sin a MDD Dai Bing ya yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki a rikicin Ukraine, su yi kokarin gaggauta kawo karshen rikicin.

Dai Bing ya bayyana yayin da yake jawabi ga Kwamitin Sulhu na MDD kan yanayin jin kai a Ukraine cewa, kasar Sin na kara kira ga dukkan bangarori masu ruwa da tsaki, da su yi la’akari da muradun jama’a, su yi kokari su inganta kawo zaman kafiya da yin iyakar kokarin ingiza dukkan bangarorin dake rikicin komawa ga tattaunawa domin gaggauta kawo karshensa.

Ya kara da cewa, tun bayan barkewar rikicin shekara guda da ta gabata, yanayin jin kai ya tabarbare. Yana mai cewa babu alamar rikicin na yin sauki, sai ma ci gaba da ake da amfani da matakan soji da manyan makamai.

Jakadan ya jaddada cewa, kasar Sin ta kasance mai kira ga bangarorin dake rikici su kiyaye dokokin jin kai na kasa da kasa da girmama rayukan mutane da kaucewa kai hari kan fararen hula da kadarorinsu da tabbatar da kwashe jami’ai da kuma kai kayayyakin agaji.

Da yake tsokaci kan cibiyoyin makamashin nukiliya, jakadan ya ce kowanne irin hatsari ka iya kai wa ga mummunar matsalar jin kai ko ta muhalli.

Game da batutuwan da suka shafi karancin abinci a duniya da makamashi da kudi kuwa, jakadan na Sin ya ce kamata ya yi dukkan bangarori su nuna sanin ya kamata su tafiyar tare da takaita bazuwar tasirin rikicin. (Fa’iza Mustapha)