logo

HAUSA

Mutane a kalla 25 sun mutu sanadiyyar wani hari a yankin Sahel na Burkina Faso

2023-02-07 10:30:15 CMG HAUSA

 

Mutane a kalla 25 sun mutu sanadiyyar wani harin ta’addanci a yankin Sahel dake arewacin Burkina Faso.

Wata sanarwar da gwamnan yankin na Sahel Lt Col. Rodolphe Sorgho ya fitar da yammacin jiya Litinin, ta ce ’yan ta’adda sun kai harin ne da tsakar ranar Asabar a unguwar Bani na yankin Seno, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane 25, wadanda suka hada da fararen hula 22 da ’yan sanda 3.

Tun cikin shekarar 2015 rashin tsaro a kasar ta yammacin Afrika ke sanadin rayuka da dama da daidaitar wasu dubbai.
Ko a makon da ya gabata, wani gwamnan da kuma rundunar soji sun bayyana cewa, a kalla mutane 28 sun mutu, cikinsu har da sojoji da fararen hula, yayin wani harin ’yan bindiga a kasar. (Fa’iza Mustapha)