logo

HAUSA

Mummunar girgizar kasa ta hallaka kusan mutane 1300 a Türkiyya da Syria

2023-02-06 21:14:20 CMG Hausa

Mutane kusan 1300 ne suka hallaka sakamakon mummunar girgizar kasa da suka auku a Turkiyya da Syria.

A cewar shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, adadin mutanen da suka rasu sakamakon girgizar kasar guda 2, da suka girgiza sassan kudancin kasar da safiyar Litinin din nan, ya kai mutum 912, yayin da wasu sama da 5,000 suka jikkata, kuma mai yiwuwa adadin ya karu yayin da ake ci gaba da zakulo mutane da gine gine suka danne.

Kaza lika ita ma ma’aikatar lafiyar kasar Syria ta ce girgizar kasar da ta auku ta hallaka mutane 371, baya ga wasu 1,089 da suka jikkata. (Saminu Alhassan)