logo

HAUSA

Girgizar kasa mai karfi ta yi sanadin rayuka 76 a Turkiye

2023-02-06 14:12:26 CMG Hausa

Kafofin watsa labarai na kasar Turkiye, sun ce mutane akalla 76 sun mutu, bayan girgizar kasa masu karfi guda biyu, sun aukawa yankunan kudanci da kudu maso gabashin kasar da sanyin safiyar yau Litinin,

Har ila yau, rahotanni daga kafofin watsa labarai na kasar Syria sun ruwaito cewa, adadin wadanda suka mutu a Syriar ya karu zuwa 111 yayin da wasu 516 suka jikkata, sanadiyyar girgizar kasar da ta auku a Turkiye. (Fa’iza Mustapha)