logo

HAUSA

Afirka ba ta bukatar lakca

2023-02-05 23:18:56 CMG Hausa

Daga Lubabatu Lei

Sakatariyar baitulmalin Amurka Janet Yellen, ta ziyarci kasashen Afirka da suka hada da Senegal, da Zambia, da Afirka ta kudu a kwanan baya, wadda kamar yadda sauran manyan jami’an kasar suka saba yi, ita ma ta zargi kasar Sin da haifar da matsalar bashi ga Zambia da sauran kasashen Afirka.

Sai dai alkaluma ba sa karya. Wani rahoton da cibiyar nazari ta "Debt Justice" ta kasar Birtaniya ta fitar a kwanan baya ya yi nuni da cewa, bisa ga kididdigar da Bankin Duniya ya yi, daga cikin basussukan da gwamnatocin kasashen Afirka suka ci, kaso 12% na kasar Sin ne, a yayin da kasashen yamma, musamman ma sassa masu zaman kansu na kasashen yamma suke binsu kaso 35%. A sa’i daya kuma, kasar Sin ta samar da basussuka ne kan kudin ruwan da bai wuce kaso 2.7% ba a duk shekara, a yayin da kudin ruwan da kasashen yamma suke karba ya kai kaso 5% a duk shekara. In mun dauki kasar Zambia ga misali, wadda bisa ga alkaluman da ma’aikatar kudi ta kasar ta samar, an ce, daga cikin basussukan da kasar ta karba, kaso 24% ne hukumomin kudi mallakar bangarori da dama suke binta, a yayin da kasashen yamma suke binta kaso 46%.

Ban da haka kuma, Sin da kasashen yamma sun sha bamban sosai, duk da cewa dukkansu na bin kasashen Afirka basussuka. Na farko, burin da suke neman cimmawa ba iri daya ba ne. Kasar Sin na ganin cewa, ainihin matsalar basussukan da Afirka ke fuskanta ita ce matsalar bunkasuwa, don haka, ta fi mai da hankali a kan tabbatar da dauwamammen ci gaban kasashen Afirka, a yayin da take samar musu basussuka, matakin da ya sa ta fi samar da basussuka a fannonin kere-kere, da ma manyan ababen more rayuwa, wadanda suka kyautata bunkasuwar tattalin arziki da rayuwar al’ummar kasashen. Misali a kasar Zambia, tashar samar da wutar lantarki da karfin ruwa da kasar Sin ta samar da kudaden jarinta, da ma gina ta tuni ta fara aiki, wadda ke iya samar da wutar da ta kai MW750, wadda ta taimaka ga rage fitar da iskar Carbon da ton dubu 663.5 a kowace shekara, baya ga kuma yadda take taka muhimmiyar rawa wurin bunkasa tattalin arziki. A sa’i daya kuma, kasashen yamma sun kasa sa kaimin bunkasuwar tattalin arzikin Afirka, har ma sun sa su kara shiga kangin talauci, kuma da hakan suke ta kara neman basussuka daga wajensu. Na biyu kuma, kasar Sin na aiwatar da hadin gwiwa da kasashen Afirka ne bisa daidaito, ba tare da tsoma baki cikin harkokin gidansu ba, don haka ma, ba ta taba gindaya sharudan siyasa a yayin da take bin su basussuka ba, sabanin yadda kasashen yamma su kan gindaya sharudan siyasa, da suka shafi hakkin bil Adam, da gyare-gyaren dokoki da makamatansu, a yunkurin tsoma baki cikin harkokin gidan kasashen bisa ga basussukan da suka samar. Na uku, kullum kasar Sin na dora muhimmanci a kan saukaka wa kasashen Afirka matsalar basussuka, ganin yadda take kokarin shiga hadin gwiwar sassa daban daban kan batun bashi, har ma ta zamanto kasar da ta fi yawan basussukan da ta tsawaita wa’adin biyansu daga cikin kasashen G20, sabanin yadda kasashen yamma suka yi shiru game da batun tsawaita wa’adin basussukan nasu sassa masu zaman kansu ke bin kasashe mafiya fama da talauci, baya ga kuma yadda suke yayata zancen wai “tarkon bashin kasar Sin” .

Da haka muna iya gano cewa, maganar wai “tarkon bashin kasar Sin”, tarko ne kasashen yamma suka kafa don lalata hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka, wanda kuma kasashen Afirka suka yi watsi da shi. Mista Emmanuel Mwamba, tsohon jakadan kasar Zambia a kungiyar tarayyar Afirka ya bayyana cewa, bai dace jami’ar Amurka ta furta kalamai masu nasaba da alakar Sin da Zambia, yayin da take ziyarar aiki a Zambia ba, domin da farko ma hakan ya sabawa da’ar ayyukan diflomasiyya, baya ga kuma yadda kamfanonin kasar Sin suka dukufa a kan gina manyan ayyuka, da suka hada da tashar samar da wutar lantarki, ya taimaka matuka ga bunkasa tattalin arziki da zaman al’umma a kasar ta Zambia.

Akwai dimbin matsalolin da kasashen Afirka ke fuskanta, kuma ba a rasa damammaki ga wadanda da gaske ne suke son taimaka wa kasashen Afirka. Wanda ke son taimaka wa kasashen Afirka daidaita matsalar basussuka, ya kamata ya dauki hakikanin matakai. Kasashen Afirka ba su bukatar lakca, kuma bai dace Amurka ta raina ’yancinsu na zabar abin da suka ga ya dace ba. (Mai zane: Mustapha Bulama)