logo

HAUSA

Tsohon shugaban kasar Pakistan Pervez Musharraf ya rasu

2023-02-05 16:41:37 CMG Hausa

A yau Lahadi ne majiyar rundunar sojojin kasar Pakistan, ta tabbatar da rasuwar tsohon shugaban kasar, kuma babban kwamandan askarawan sojojin kasar Pervez Musharraf.

Majiyar ta ce Musharraf ya rasu ne a wani asibiti dake Dubai, bayan ya sha fama da jinya. Kaza lika ta ce jagorancin rundunar sojin kasar na matukar alhinin rasuwar tsohon shugaban.

An haifi Musharraf ne a ranar 11 ga watan Agustan shekarar 1943, ya kuma shugabanci Pakistan tsakanin shekarar 2001 zuwa 2008.

Rahotanni daga wasu kafofin watsa labaran kasar sun ce za a mayar da gawarsa gida, domin yi masa jana’iza tare da binne shi.  (Saminu Alhassan)