logo

HAUSA

Mutanen Zinder na nuna damuwa sosai game da tsadar kayayyakin abinci a cikin kawuwanni

2023-02-04 18:23:26 CRI

 Tun lokacin da majilisar dokokin kasar Nijar ta rattaba hannu da babban rinjaye kan kasafin kudin shekarar 2018, ’yan kasar Nijar suka fara ji a jikinsu, inda tun daga lokacin kome ya kara, lamarin da ya janyo hauhawar farashin kayayyakin abinci da kuma kayayyakin bukatun yau da kullum. Baya ga wannan matsalar annobar Covid-19 da rikicin Ukraine ta kara saka ’yan Nijar cikin halin Rabbana ka wadata mu, duk da kokarin da gwamnatin kasar take yi kawo saukin rayuwa ga ’yan kasarta ta hanyar ba da taimakon abinci da saida cimaka a farashi mai rahusa a cikin yankunan karkara da birane na jihohin Nijar guda takwas. A yankin Zinder, duk da girbin damanar bana, mutane suna fama da tsadar rayuwa da hauhawar farashin kayan abinci, lamarin da ya tura kungiyoyin kare masu saye da sayarwa yin kira ga ’yan kasuwa da hukumomin wurin da su dubi talakawa da idon basira.

A Jamhuriyar Nijar duk da cewa tsadar rayuwa da hauhawar farashin kayan abinci sun samo asili ne a cewar wasu masu fashin baki, daga annobar covid 19 da rikicin Ukraine, yankin Zinder na daya daga cikin yankunan kasar guda takwas da mutane suka rasa tudun dafawa game tsadar abincin da sauransu. Sai dai wasu na ganin wannan matsala ta tsadar rayuwa ta kunno kai hasalima bayan kada kuri’ar amincewa ta ’yan majalisa kan ayar dokar kasafin kudin shekarar 2018. Amadou Mamane Dan Kore, mairajin kare hakkin dan Adam na fararen hula, ya tabbatar da cewa kayayyakin abinci sun kara kudi.

Ni yanzu da rabona na sayi shinkafa jika goma da rabi har ma na mance. Shinkafa daga abin da nike sanyenta daga jika goma sha abin da ya yi sama, da na kara komawa ma aka ce mini ta kai jika goma sha uku. Kuma sai ka zo aka dora haraji bisa abin da ya shafi man girki, bisa abin da ya shafi shinkafa, bisa abin da ya shafi madara, to yaya ne za ka ganin wadannan abubuwan ba za su yi tashin gwabron zabo a kasuwa ba.

Alhaji Abou Ousmane, mamba na kungiyar ’yan kasuwar jihar Zinder, ya bayyana cewa ’yan kasuwa bita da kulli ake musu.

Duka shi wannan kasuwancin da dan kasuwa shi ke yi a cikin jihohin Nijar gaba daya. Gwamnatin ta san abin da dan kasuwa yake sayo kaya daga wurin sayen kaya. Farashi ba kullum ba yake zamantowa daya, wani lokacin sai a samun farashin ya hau, wani lokacin sai a samu ya sauka. Amma wannan lokacin da aka shigo cikin zamanin da ake babu maganar farashi ya sauka, kullum cikin halin kari yake. Kuma wallahi cikin halin da ake ciki idan ka saida yau, gobe idan Allah ya kai mu ka koma kasuwa sai ka cika za ka sayen wani, halin da muke ciki ke nan. Dan kasuwa idan ka dubi ka gani fa, saboda Allah, saboda Annabi, a matsayin da ake ciki a yanzu, wallahi dan kasuwa yana taimakawa.

Sai dai a cewar Amadou Mamane Dan Kore.

Dole ne, za a zo a zauna da ’yan kasuwa da ita gwamnati, ya zamanto a san yaya ne za a yi, a gani tun da ita gwamnati akwai abubuwan da ya kamata ta rage musu, su kuma ’yan kasuwa ya kamata su yi adalci. Kundin tsarin mulki kwatantawa ya yi mu so muke mu dora jamhuriya, wanda take da tausayin al’umma.

Mai da gaskiya ga noma da kiwo da kuma kasuwanci, ita ce hanyar tsira ga duk wata kasar da ke neman ci gaba.

Mamane Ada, sashen hausa na CRI daga Yamai, a jamhuriyar Nijar.