logo

HAUSA

Wasu bata-gari sun kone ofishin hukumar zabe dake jihar Anambra a kudancin Najeriya

2023-02-02 10:30:31 CMG Hausa

Kakakin rundunar ’yan sanda a jihar Anambra dake kudancin Najeriya Tochukwu Ikenga, ya ce wasu bata-gari sun kone ofishin hukumar zabe mai zaman kan ta INEC, tare da kaddamar da hari kan wani ofishin ’yan sanda dake daura da wurin, a yankin Ojoto na karamar hukumar Idemili ta kudu.

Ikenga, wanda ya tabbatar da aukuwar harin na jiya Laraba, yayin da yake zantawa da manema labarai a birnin Onitsha, ya ce maharan sun hallaka mutum guda, tare da jikkata karin wani mutumin na daban. Ya ce tun da fari maharan sun isa ofishin hukumar ta INEC ne cikin wasu kananan motoci kirar bas, sannan suka yi amfani da ababen fashewa da fetur su kone ofishin. Daga nan ne kuma suka kai farmaki kan ofishin ’yan sandan dake kusa, da ma wani gida na farar hula dake daura da wurin.

A baya bayan nan dai ana yawan kaiwa ofisoshin hukumar INEC hari, a wasu yankuna na kudu maso gabashin Najeriya, yayin da babban zaben kasar ke kara karatowa. (Saminu Alhassan)