logo

HAUSA

WHO:Cutar COVID-19 na kan matsayin ko-ta-kwana

2023-02-01 19:50:47 CMG Hausa

A ranar Litinin, hukumar lafiya ta duniya WHO, ta bayyana cewa, cutar COVID-19 na ci gaba da kasancewa batun gaggawa a fannin kiwon lafiya, wanda ke jan hankalin sassan kasa da kasa, ta yadda kasashen duniya ke jiran ko-ta-kwana.

WHO ta kara da cewa, akwai yiwuwar annobar COVID-19 ta kasance a wani yanayi na haifar da illa ga duniya, duk da cewa a bana, duniya ta samu sauki, idan an kwatanta da makamancin lokaci a bara, yayin da nau’in Omicron na cutar ke kan ganiyar bazuwa. (Alhassan Saminu)