logo

HAUSA

NATO ba za ta iya tasiri a yankin Asia da Pasifik ba

2023-02-01 16:27:12 CMG Hausa

Sakatare Janar na kungiyar tsaro ta NATO Jens Stoltenberg dake ziyara a Japan, da firaministan  kasar Fumio Kishida, sun fitar da wata sanarwar hadin gwiwa a jiya, inda bangarorin biyu suka lashi takobin hada gwiwa a bangarorin tsaron ruwa da intanet da takaita yaduwar makamai da sauran wasu fannoni, yayin da suka ambaci karfin sojin kasar Sin da batun Taiwan.

Karkashin kawancen Amurka da ake kira da Indo-Fasifik, wato na kawancenta da kasashen yankin tekun Indiya da Fasifik, NATO da ta samo asali daga yakin cacar baka, ta baza komarta zuwa yankin Asiya da Fasifik domin fakewa da kasar Sin, da haifar da yakin cacar baka. Wannan yunkuri na matukar bukatar kasashen yankin Asiya da Fasifik su sa masa ido sosai.

NATO babbar kungiyar kawancen tsaro ce a duniya mai tarin laifuffuka. Tun bayan kafuwarta, ta kasance wani makami da Amurka ke amfani da shi wajen kafa rukunonin kawance da yin fito-na-fito. A yau, NATO ta sauya. Bayan kawo karshen yakin cacar baka, a hankali ta rikide daga kawancen soji zuwa na siyasa da diflomasiyya, haka kuma karfin ayyukanta ya yi ta raguwa, kana mambobinta da dama na fuskantar karancin kudi. Mafiya yawan kasashe a yankin Asia da Pasifik sun fahimci shirin NATO da Amurka na karkatar da ruwa zuwa yankin gabashi, kuma sun bayyana rashin amincewarsu.   

NATO a yanzu ba ta da wani tasiri, kuma ranakunta kirgaggu ne.(Fa’iza Mustapha)