logo

HAUSA

Shinkafar da aka tagwaita irin ta na samar da damar taimakawa Afirka wajen kaucewa kamfar abinci

2023-01-29 16:16:33 CMG Hausa

Shugaban ofishin tsara shirye shirye, da bunkasa cinikayya a cibiyar raya fasahohin noma ta Afirka ko AATF Emmanuel Okogbenin, ya ce rungumar noman shinkafar da aka tagwaita halittar irin ta, zai samar da wata dama ga nahiyar Afirka, ta jurewa mummunan tasirin yanayi.

Masanin kimiyyar ya ce, wannan iri na shinkafa na da juriyar kwari da sauran cututtukan shuka, don haka zai taimaka sosai wajen dakile kamfar abinci, da samar da abinci mai gina jiki ga sassan nahiyar Afirka.

Emmanuel Okogbenin, wanda ya bayyana hakan a ranar Juma’a, ya kara da cewa, bunkasa noman nau’in shinkafar, zai fadada ikon Afirka na kaucewa yunwa da shawo kan fatara a yankunan karkarar Afirka. Ya ce "Muna karfafa gwiwar manoma da su rungumi wannan nau’i na shinkafa, wanda ke samar da yabanya mai yalwa, kuma yake jura yanayi daban daban, kana tana ba da zarafin samar da isasshen hatsi, da riba ga mazauna karkara.

Okogbenin ya yi tsokacin ne yayin ziyarar gani da ido, a yankin gonakin noman rani na Mwea dake tsakiyar kasar Kenya, inda cibiyar AATF ke jagorantar shirin gwajin juriyar nau’in noman shinkafar da aka tagwaita irin ta, domin tantance ko za ta iya jure yanayi mai tsanani, da illar kwari, da kuma cututtukan shuka. (Saminu Alhassan)