logo

HAUSA

Shugaban Senegal ya yi kira da a kara kaimin zakulo dabarun shawo kan matsalar kamfar abinci a Afirka

2023-01-26 17:01:45 CMG Hausa

Shugaban kasar Senegal Macky Sall, ya ja hankalin shugabannin kasashen Afirka, da su yi tsayin daka wajen zakulo dabarun ‘yantar da nahiyar daga kamfar abinci. Shugaba Macky Sall, ya yi tsokacin ne yayin taron koli karo na 2 na Dakar, wanda ke maida hankali ga tattauna matakan shawo kan matsanancin kalubalen kamfar abinci dake tunkarar Afirka.

Shugaban na Senegal ya kara da cewa, ‘yancin ciyar da Afirka ya zama batun gaggawa, a gabar da kasashen nahiyar ke shan fama da hadakar mummunan tasirin sauyin yanayi, da bazuwar annobar COVID-19, da wasu tashe tashen hankula. Ya ce a wannan yanayi da ake ciki, ya kamata kasashen Afirka su rungumi dawainiyar ciyar da kan su da ma samar da taimako wajen ciyar da sauran sassan duniya, duba da cewa nahiyar na da ikon yin hakan.

A nasa jawabin, shugaban bankin raya Afirka na AfDB, Mr. Akinwumi Adesina, ya bayyana aniyar bankin sa na fitar da kudin da yawan su zai kai dalar Amurka biliyan 10, domin bunkasa harkokin noma, da ‘yantar da Afirka a fannin ciyar da kai.

Mr. Adesina ya ce ya zama wajibi taron na Dakar, ya samar da damar ingiza sabon mafarin cimma nasara a fannin noma, duba da cewa nahiyar Afirka ce ke da kaso 65 bisa dari, na filayen noma dake duniya. To sai dai duk da hakan ya bayyana damuwa, ganin yadda nahiyar ke dogaro da hatsin da ake shigowa da shi daga waje, yayin da miliyoyin al’ummun nahiyar ke kwana da yunwa.

An dai bude taron Dakar na yini uku ne a jiya Laraba, kuma bankin AfDB, da gwamnatin Senegal ne suka dauki nauyin gudanar da shi.  (Saminu Alhassan)