logo

HAUSA

Sinawa a Kano sun gudanar da bikin sabuwar shekarar Zomo

2023-01-22 16:53:06 CMG Hausa

Ranar Asabar 21 ga wata ’yan kasar Sin mazauna Kano dake arewacin Najeriya sun bi sahun sauran takwarorin su na duniya wajen sheda bikin murnar sabuwar shekarar gargajiya ta kasar Sin.

Sun dai gudanar da kwarya-kwaryar bikin ne a wani gidan abinci mai suna RED-CHINA dake unguwar Nasarawa GRA a birnin na Kano.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Wannan dai shi ne karo na farko cikin shekaru uku da Sinawan suka samu damar sheda bikin sabuwar shekarar, wanda a baya suka gaza yin hakan saboda annobar Covid-19 da ta addabi duniya.

Akasarin mahalarta bikin ’yan kasuwa ne da suke gudanar da harkokin kasuwancinsu daban daban a birnin na Kano sai kuma abokan huldar da su ma suka zo domin taya su murna.

Mr. Pu Mao wanda wannan shi ne karonsa na farko a tarihi da ya taba gudanar da bikin sabuwar shekarar a wata kasa.

“Kamar dai kowacce shekara muna samun wata rana guda daya da take da mahimmanci ga duk wani Basine, wato dai sabuwar shekarar Sinawa ke nan, to amma fa kowane dan kasar Sin yana gudaanr da shagalin bikin wannan rana ce a cikin iyalansa, to sai dai mu yanzu ga shi muna namu bikin a wata kasa, gaskiya dai abin akwai dan damuwa kadan  wannan shi ne karo na farko da na taba sheda bikin sabuwar shekarar a wata kasa ba tawa ba, ni na fito ne daga lardin HAINAN.”

Shi kuwa Mr Ye cewa yake, “Muna fatan a wanann sabuwar shekarar komai zai iya sauyawa musamman ma batu tattalin arziki muna son al’amura su daidaita.”

Iyalan Sinawan dai dake birnin na Kano sun fara gudanar da shagalin murnar sabuwar shekarar ce tun daga Juma’a 20 ga wata, sun kuma kasance cikin walwala da natsuwa, inda suka yi amfani da wanann dama wajen yiwa Najeriya fatan samu bunkasuwar arziki da zaman lafiya. Daga tarayyar Najeriya, Garba Abdullahi Bagwai, CRI Hausa. (Garba Abdullahi Bagwai)