logo

HAUSA

Bankin CBN ya fara shiga kasuwanni domin wayar da kan ’yan kasuwa

2023-01-19 09:16:20 CRI

A ranar Laraba 18 ga wata, jami’an babban bankin tarayyar Najeriya CBN suka kaddamar da gangamin wayar da kan ’yan kasuwa a babbar kasuwar garin Sokoto dake arewacin kasar game da wa’adin daina amfani da tsoffin takardun kudi.

Gangamin dai ya zo ne dai-dai lokacin da ya rage kwanaki 13 dokar hana amfani da tsoffin takardun kudin ya fara aiki gadan gadan a kasar.

Tun dai a watanni biyu da suka gabata ne babban banki kasa na CBN ya sanar da sauya fasalin takardun kudi na Naira dubu 1 da kuma Naira dari 5 kana da Naira dari 2 a wani mataki na kara farfado da darajar Naira da dakile almundahar kudade a tsakanin al`ummar kasar.

Tuni dai wadannan sabbin kudade suka fara wanzuwa a bankunan kasuwanci dake sassa daban daban na Najeriya, bayan da aka tsayar da ranar 31 ga wata Janairu a matsayin lokacin da gaba daya za a janye tsoffin kudaden daga hannun al’umma.

A yayin gangamin a babbar kasuwar dake garin Sokoto a arewacin Najeriya jami’in bankin na CBN shiyyar Sokoto Alhaji Dahiru Usman ya ce ya zamarwa bankin wajibi ya dukufa wajen wayar da kan ’yan kasuwa  shirin daina amfani da tsoffin kudaden da kuma tsarin nan na E-Naira wanda zai maye gurbin amfani da tsabar kudi wajen hada-hadar kasuwanci.

“Wannan taron zai baiwa ’yan kasuwa damar sanin dalilan gwamnati na samar da sabbin kudade, sannan kuma ya ba su damar sanin muhimmancin manhajar E-Naira wajen gudanar da harkokin saye da sayarwa bayan nan kuma taron zai kawar da rade-radin da ake yadawa cewa wai bankin na CBN ya kara tsawaita lokacin daina amfani da tsoffin kudin, ba a Najeriya aka fara wannan tsarin ba a don haka ba gudu ba ja da baya.”

Shugabannin ’yan kasuwa da kungiyoyin hada-hadar kudade ne suka samu halartar  taron wayar da kan, inda da yawansu suka nuna bukatar a kara tsawaita lokacin daina amfani da tsoffin kudin.

“Wannan tsari kamata ya yi a ce zai shafi manyan ’yan kasuwa ne kawai masu juya kudin da ya haura miliyan 3, amma kamata ya yi a daga kafa ga kananan ’yan kasuwa, muna mu’amulla ne da mutanen da suka fito daga kauyuka bai dace a tilasta cewa 31 ga wata za a dakatar da amfani da tsoffin kudaden ba.”

“Alhaji Abubakar Atiya shugaban kungiyar ’yan kasuwa na babbar kasuwar Sokoto. Hakika babban bankin kasa na CBN  ya yi kokari sosai domin ya gaya mana gaskiyar lamari a kan jita-jitar da ake yadawa cewa za a kara wa’adi, a sabo da haka mu yanzu ya zamar mana wajibi mu himmatu a matsayinmu na shugabannimu wayar da kan ’yan kasuwarmu su hanzarta musanya kudadensu kafin karewar wa’adin don gudun asara tun da gwamnati ba ta da niyyar dibar wasu sabbin kwanaki daga ranar 31 ga wannan wata.”

A yayin gangamin wakilan babban bankin na CBN sun kwadaitawa ’yan kasuwa irin garabasar dake tattare da amfani da manhajar E-Naira wajen gudanar da harkokin saye da sayarwa wanda yanzu duniya ke alfahari da shi. (Garba Abdullahi Bagwai)