logo

HAUSA

Dai Bing: Ta hanyar tattaunawa ne kadai za a iya kaiwa ga warware rikicin Ukraine

2023-01-18 11:49:52 CMG Hausa

Mataimakin wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Dai Bing, ya ce tattaunawa ce kadai hakikanin hanyar warware rikicin kasar Ukraine. Yayin da yake jawabi a zaman kwamitin tsaron MDD na jiya Talata game da rikicin kasar ta Ukraine, Dai Bing ya ce kamata ya yi sassan kasa da kasa, su karfafawa Rasha da Ukraine gwiwar komawa teburin shawara, da rungumar ka’idojin gaggauta dakatar da bude wuta da tashin hankali.

Dai Bing ya ce "Ya kamata a yi watsi da duk wani furuci na ruwa wutar kiyayya, da matakan dake haifar da zaman doya da man ja. A wannan gaba, kamata ya yi a yi amfani da gudummawar addini domin karfafa hadin kai, da gina burin zaman lafiya a zukatan al’ummun sassan biyu".

Jami’in na Sin ya kara da cewa, har kullum kasar sa na tsayawa kan akidar martabawa, da kare hakkin gudanar da addinai, tare da fatan karfafa yin musaya tsakanin addinai, da kimanta juna, da wanzar da al’adar zaman lafiya, ta yadda hakan zai ingiza karsashin warware batutuwan siyasa masu sarkakiya.

Bugu da kari, Dai ya ce Sin za ta ci gaba da goyon bayan adalci, da rashin nuna banbanci, kana za ta yi aiki da dukkanin kasashe masu son zaman lafiya, wajen gina tsarin daidaito a duniya, da taka rawar gani a fannin warware rikicin Ukraine lami lafiya.   (Saminu Alhassan)