logo

HAUSA

Majalissar wakilan Amurka ta zabi sabon kakaki bayan danbarwar siyasa mafi tsanani a tarihi

2023-01-08 15:19:12 CMG Hausa

Da safiyar Jiya Asabar ne majalissar wakilan kasar Amurka, ta cimma nasarar zaben Kevin McCarthy a matsayin kakakin ta, bayan shafe kwanaki ana danbarwa kan wanda zai dare kujerar jagorancin majalissar.

Dan majalissa McCarthy na jami’iyyar Republican daga jihar California, ya cimma nasarar samun isassun kuri’un zama sabon kakakin majalissar ne, a zagaye na 15 na kada kuri’a, wanda shi ne zagaye mafi tsayi da aka kai kafin zaben kakakin majalissar ta wakilan Amurka cikin shekaru 164 a tarihin kasar. Kuma rabon da a gaza zaben sabon kakakin majalissar wakilan Amurka a zagayen jefa kuri’a na farko yau da shekaru 100.

Shugaban Amurka Joe Biden na jam’iyyar Democrat, ya bayyana a farkon makon da ya gabata cewa, gaza cimma nasarar zaben kakakin majalissar wakilan Amurka a kan lokaci abun kunya ne ga kasar, domin hakan ya dakatar da gudanar harkokin majalissar bisa doka yadda ya kamata.

Daukacin ‘ya’yan jami’iyyar Democrats dai sun zabi Hakeem Jeffries na jam’iyyar su daga birnin New York ne, matakin da ya sanya shi zama sabon shugaban marasa rinjaye, kuma dan asalin Afirka na farko a tarihin Amurka, da zai jagoranci jam’iyyar sa, a daya daga cikin majalissun dokokin Amurka guda 2.  (Saminu Alhassan)