logo

HAUSA

Ziyarar da shugaban Philipphines ya kawo Sin a sabuwar shekara tana da babbar ma’ana

2023-01-05 21:44:08 CMG Hausa

Daga shawarar ziri daya da hanya daya, da aikin gina, da kamun kifi, da kayayyakin more rayuwa, da harkokin kudi, zuwa yawon bude ido, na daga cikin jerin muhimman takardun hadin gwiwa da shugabannin kasashen Sin da Philippines suka shaida sanya hannu a kai. Wannan jerin sakamako da aka cimma, sun shaida abubuwan da ba a saba gani ba yayin ziyarar da wani shugaban wata kasa ya kawo kasar Sin a sabuwar shekara.

A jiya ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi shawarwari da takwaransa na kasar Philippines Ferdinand Marcos a birnin Beijing, wanda ya kawo ziyarar aiki a kasar Sin.

Shugabannin biyu sun jaddada muhimmancin huldar dake tsakanin kasar Sin da Philippines, sun kuma amince su ci gaba da yin shawarwari bisa manyan tsare-tsare, da cimma matsaya mai muhimmanci kan zurfafa hadin gwiwa a aikace, da daidaita al'amuran teku yadda ya kamata.(Ibrahim)