logo

HAUSA

Kasashe 5 sun fara aiki a matsayin sabbin zababbun mambobin kwamitin sulhun MDD

2023-01-04 20:53:44 CMG Hausa

A jiya ne kasashe biyar, da suka hada da Ecuador, da Japan, da Malta, da Mozambique da Switzerland, suka fara aiki a matsayin mambobi da ba na dindindin ba a kwamitin sulhun MDD

A ranar 1 ga watan Janairun shekarar 2023 ne, wa'adinsu na tsawon shekaru biyu ya fara aiki a hukumance, amma jiya Talata 3 ga wata, shi ne zaman farko na kwamitin na sulhu na shekarar 2023, bayan hutun sabuwar shekara.(Ibrahim)