logo

HAUSA

Mutane miliyan 100 sun rasa muhallansu a 2022

2022-12-27 13:26:05 CMG Hausa

Hukumar kula da ’yan gudun hijira ta MDD (UNHCR), ta ce mutane miliyan dari a fadin duniya ne suka bar matsugunansu bisa tilas a shekarar 2022, yayin da MDD ke ci gaba da taimakawa mabukata ta hanyoyi daban-daban.

Shugaban hukumar UNHCR Flippo Grandi, ya bayyana adadin a matsayin matakin da bai kamata a cimma ba.

Adadin ya karu ne kan miliyan 90 da ya kasance a shekarar 2021. Barkewar sabbin rikice-rikice ko wadanda suka dauki lokaci mai tsawo ne, muhimman abubuwan dake sabbaba kaura a sassa daban-daban na duniya, ciki har da Ukraine da Habasha da Burkina Faso da Syria da Myanmar.

Sashen yada labarai na MDD ya yi gargadin cewa, dubban mutane dake cikin matsi ne ke ganin Turai a matsayin wuri mafi dacewa su je, inda suke sanya rayukansu cikin hadari a hannu masu safarar mutane da bin hanya mai hadari ta tekun Bahr Rum. (Fa’iza Mustapha)