logo

HAUSA

Argentina ta sanar da hutun yini daya a fadin kasar don murnar lashe kofin kwallon kafan duniya

2022-12-20 11:23:25 CMG Hausa

Gwamnatin Argentina ta sanar da hutun kwana daya a kasar a jiya, don murnar lashe kofin gasar cin kofin kwallon kafa na FIFA da aka kammala a Qatar.

Rahotanni na cewa, yau da safe ne, ake sa ran tawagar ’yan wasan Argentina za ta isa Buenos Aires, babban birnin kasar, inda shugaban kasar zai tarbe su a yau din, daga bisani kuma gwamnatin kasar za ta shirya musu wani gagarumin bikin taya murna a hukumance. (Safiyah Ma)