logo

HAUSA

Jakadan Sin ya gana da sakataren baitulmalin Amurka

2022-12-16 20:08:35 CMG Hausa

Jakadan kasar Sin dake Amurka Qin Gang, ya gana da sakataren baitulmalin Amurka Janet Yellen a jiya Alhamis, inda jami’an biyu suka tattauna game da yadda za a aiwatar da shawarwarin da shugabannin kasashen 2 suka cimma a baya bayan nan, kamar dai yadda ofishin jakadancin Sin dake birnin Washington ya tabbatar.

Kaza lika manyan jami’an biyu sun amince da ci gaba da tuntubar juna yadda ya kamata.  (Saminu Alhassan)