logo

HAUSA

An rufe taron kolin EU bayan amincewa da kakabawa Rasha takunkumi zagaye na tara

2022-12-16 10:40:50 CMG Hausa

An rufe taron kolin EU na lokacin hunturu a Brussel, babban birnin kasar Belgium da daren jiya bisa agogon wurin. Shugaban majalisar zartaswa ta EU Charles Michel, ya bayyana a gun taron manema labarai da aka gudanar bayan taron kolin cewa, shugabannin kasashen EU sun amince da shirin kakabawa Rasha takunkumi zagaye na tara. Bisa tsarin, ana bukatar tantance shirin ta hanyar “rubuttatun hanyoyin” a yau.

Bugu da kari, a cikin taron kolin a wannan rana, shugabannin kasashen EU sun amince da ba da tallafin tattalin arziki na euro biliyan 18 a hukumance ga Ukraine a shekarar 2023. A sa’i daya kuma, an amince da Bosnia da Herzegovina a matsayin 'yan takarar neman shiga Tarayyar Turai a hukumance. (Safiyah Ma)