logo

HAUSA

Kasar Sin Za Ta Goyi Baya Da Taimakawa Somaliya Wajen Sake Gina Kasar Da Yaki Da Ta'addanci

2022-12-09 20:02:12 CMG HAUSA

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana a Jumma'ar nan cewa, a shirye kasar Sin take ta ba da taimako gwargwadon karfinta, don sake gina kasar Somaliya, da raya zamantakewar al'umma da tattalin arziki na Somaliya, kuma tana karfafa gwiwar kamfanonin kasashen biyu, da su yi kokarin yin hadin gwiwa a sassan da suka hada da aikin gona, da kamun kifi da kiwon lafiya.

Shugaba Xi ya bayyana haka ne, lokacin da yake ganawa da takwaransa na kasar Somaliya Hassan Sheikh Mohamud. Yana mai cewa, kasar Sin tana goyon bayan gwamnatin Somaliya, wajen kara karfinta na tabbatar da zaman lafiya da yaki da ta'addanci. (Ibrahim)