logo

HAUSA

Guterres ya yaba da yarjejeniyar warware rikicin Sudan

2022-12-06 09:27:54 CMG Hausa

Babban magatakardar MDD Antonio Guterres, ya yi na’am da yarjejeniyar cimma daidaito, tsakanin sojojin gwamnatin kasar Sudan da ‘yan siyasar kasar.

Cikin wata sanarwa da ofishin sa ya fitar a jiya Litinin, Mr. Guterres ya yi fatan yarjejeniyar za ta share fagen mika mulki ga zababbiyar gwamnatin farar hula a kasar. Ya kuma yi kira ga daukacin masu ruwa da tsaki a harkokin siyasar Sudan, da su yi aiki tukuru wajen ganin an warware muhimman batutuwan siyasar kasar, domin kaiwa ga cimma matsaya mai dorewa a siyasance, wadda dukkanin sassa za su aminta da ita.

Guterres ya kara da cewa, MDD da hadin gwiwar tawagar dake fafutukar tallafawa mika mulki ga farar hula a Sudan, da kungiyar IGAD, suna kara himmatuwa, wajen ganin sun tallafawa nasarar wannan muhimmin aiki.    (Saminu Alhassan)