logo

HAUSA

UNICEF ya kaddamar da asusun tallafawa yaran dake yankin kahon Afirka

2022-12-06 09:52:55 CMG Hausa

Asusun tallafawa kananan yara na MDD ko UNICEF, ya kaddamar da asusun gaggawa na neman taimakon dalar Amurka biliyan daya, domin tallafawa yaran dake rayuwa a sassan yankin kahon Afirka a shekarar 2023 dake tafe.

UNICEF wanda ya kaddamar da asusun na musamman a jiya Litinin, ya ce ya sake nazartar kudaden tallafin gaggawa na jin kai da ake bukata, domin kare rayuwar yara dake kasashen Habasha, da Kenya da Somaliya, inda adadin kudaden da ake bukata domin gudanar da ayyuka ya sauya, daga dala miliyan 879 a watan Satumba zuwa dala biliyan daya a shekara mai zuwa.

Kaza lika asusun na UNICEF, ya ce yaran dake yankin kahon Afirka na fuskantar mawuyacin halin rayuwa, sakamakon mummunan fari da aka jima ba a ga irin sa ba a tarihin kasashen 3, tare da tashe tashen hankula dake ci gaba da addabar arewacin Habasha.

Da take tsokaci kan hakan, cikin wata sanarwa da ofishin ta ya fitar, babbar daraktar UNICEF Catherine Russell, ta ce mummunan tasirin sauyin yanayi na barazana ga rayukan yara, kuma hakan ne ya sanya asusun dora muhimmancin gaske, ga dabarun jurewa da iya rayuwa tare da tasirin sauyin yanayi, a matsayin muhimman bangarorin tallafin jin kai da yake aiwatarwa.

Jami’ar ta ce hakan zai taimaka matuka, wajen kaiwa ga yaran dake rayuwa cikin yanayin tashe tashen hankula, tare da ba da damar taimaka musu, da al’ummun su shiryawa abubuwan daka iya aukuwa a nan gaba.  (Saminu Alhassan)