logo

HAUSA

Tsarin mabambanta halittu na duniya bayan shekarar 2020 shi zai zama babban taken babban taron MDD

2022-12-06 20:27:33 CMG HAUSA

 

Amincewa da tsarin mabambantan halittu na duniya bayan shekarar 2020, shi ne kan gaba a ajandar babban taron MDD da ke tafe, a gabar da duniya ke fuskantar asarar nau'o’in halittu mafi girma a duniya, tun bayan bacewar dabbar dinosaur a doron kasa.

Sakatariyar zartarwa mai kula da yarjejeniyar mabambantan halittu a duniya ta MDD Elizabeth Maruma Mrema, ta fadawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua gabanin kashi na biyu na taron sassa da suka sanya hannu kan yarjejeniyar karo na 15 (COP15) da aka shirya gudanarwa a ranar 7 zuwa 19 ga watan Disamba a Montreal na kasar Canada cewa, babu wata duniya ta biyu ko duniyar B.

Jami’ar ta bayyana a ciki wata sanarwa cewa, ana sa ran za a fito da sabon tsarin mabambantan halittu na duniya tare da bukatun cimma wani buri da takamaiman manufa, don ganin an kai ga cimma sauyi a tsakiyar karni.(Ibrahim)