logo

HAUSA

Sakatare Janar na MDD ya yi kakkausar suka kan harin da aka kai wa filin jirgin saman Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

2022-11-27 16:55:19 CMG Hausa

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya António Guterres, ya fitar da sanarwa ta bakin kakakinsa a jiya Asabar, inda ya yi kakkausar suka kan harin da aka kai wa filin jirgin sama dake yankin kudu maso gabashin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

Da safiyar ranar Alhamis ne aka kaddamar da hari kan filin jirgin sama na Obo da ke Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, wanda ke kusa da kan iyakar Kongo (Kinshasa) da Sudan ta Kudu, inda aka kashe wani sojan kiyaye zaman lafiya na kasar Morocco.

Tawagar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ko (MINUSCA), ta ce ta riga ta fara gudanar da bincike kan yadda lamarin ya faru. (Mai fassara: Bilkisu Xin)