logo

HAUSA

An shirya bikin tunawa da iyali kan kisan kiyashin da aka yi Nanjing

2022-11-25 20:02:55 CMG Hausa

A yau ne, aka kaddamar da bikin tunawa da iyalan wadanda aka halaka a birnin Nanjing, babban birnin lardin Jiangsu dake yankin gabashin kasar Sin.

Bikin tunawa da iyalin na zuwa ne makwanni 2 gabanin ranar da kasar Sin ke bikin tunawa da wadanda aka kashe a kisan kiyashin da ya faru a birnin na Nanjing karo na 9 a ranar 13 ga watan Disamba.

A ranar 13 ga watan Disamban shekarar 1937 ne, sojojin Japan suka mamaye birnin Nanjing, babban birnin kasar Sin a wancan lokaci. A tsawon sama da makonni 6, maharan kasar Japan sun halaka Sinawa fararen hula da sojojin da ba sa dauke da makamai sama da dubu 300. (Ibrahim)