logo

HAUSA

Yawan wadanda suka mutu sanadiyyar girgizar kasa a Indonesia ya karu zuwa 162

2022-11-22 10:47:38 CMG Hausa

 


Jimilar mutane 162 ne suka mutu, bayan girgizar kasa mai karfin maki 5.6 ya aukawa lardin West Java na Indonesia.

Jami’ai sun ce girgizar ta kuma yi sanadin lalacewar gidaje da gine-gine da kayayyakin more rayuwa. An kuma ji girgizar sosai a Jakarta, babban birnin kasar.

Hukumar kula da ayyukan agaji da shawo kan iftila’i ta gundumar Cianjur, daya daga cikin wuraren da iftila’in ya fi tsanani, ta ce girgizar ta tilastawa kimanin mutane 13,784 tserewa domin neman mafaka, saboda lalacewar gidajensu. (Fa’iza Mustapha)