logo

HAUSA

Shugaban Cuba zai kawo ziyarar aiki kasar Sin

2022-11-21 18:52:40 CMG Hausa

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying, ta sanar Litinin din nan cewa, sakataren farko na kwamitin kolin Jam’iyyar kwaminis ta kasar Cuba, Miguel Diaz-Canel, zai kawo ziyarar aiki kasar Sin daga ranar 24 zuwa 26 ga watan Nuwanban da muke ciki, bisa gayyatar da Xi Jinping, babban sakataren kwamitin kolin JKS kana shugaban kasar Sin ya yi masa. (Ibrahim)