logo

HAUSA

Sakatare janar na MDD na neman a dauki kwakkwaran mataki kan batun sauyin yanayi

2022-11-19 16:31:46 CMG Hausa

Sakatare janar na MDD Antonio Guterres, na neman a dauki kwakkwaran mataki, yayin da ake gab da rufe taron koli kan sauyin yanayi na MDD ko COP27 dake gudana a kasar Masar. 

Farhan Haq, mataimakin kakakin MDD, ya bayyana jiya cewa, Antonio Guterres ya gana a mabambantan lokuta, da kasashe mambobin kungiyar Tarayyar Turai (EU) da mambobin kungiyar kasashe maso tasowa 77 da kasar Sin da kuma mataimakin shugabar hukumar EU Frans Timmermans da manzon musammam na kasar Sin kan sauyin yanayi, Xie Zhenhua, a birnin Sharm El Sheikh na Masar.

Sakatare Janar din ya bukaci dukkan bangarori su cimma yarjejeniya kan ingantattun manufofin kawar da asara da illolin sauyin yanayi da rage fitar da iska mai guba. Yana mai cewa, hakika wannan yarjejeniya, kamar kowacce, za ta zama sakamako na hakuri da wasu batutuwa, kuma suna fatan za ta haifar da sakamako mafi karfi, wajen tabbatar da kokarin dakatar da dumamar yanayi.

Bugu da kari, Antonio Guterres ya bukaci bangarorin dake halartar taron, su daina nunawa juna yatsa. Inda ya bukaci sun mayar da hankali kan batutuwa 3 da suka hada, daukar mataki kan illoli da asarar da sauyin yanayi ya haifar, da cike gibin rage iska mai guba, da samar da kudaden tunkarar sauyin yanayi. (Fa’iza Mustapha)