logo

HAUSA

Iran ta yi fatali da daftarin dake neman baiwa IAEA hadin kai

2022-11-17 10:44:01 CMG Hausa

Shugaban hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasar Iran Mohammed Eslami, ya bayyana cewa, daftarin kudurin dake adawa da kasarsa da aka shirya amincewa da shi a taron da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya (IAEA) da ake gudanarwa, ba shi da sahihanci, kuma Iran ta yi watsi da shi.

Eslami ya bayyana haka ne ga manema labarai, a gefen taron majalisar ministocin kasar, yayin da yake mayar da martani ga taron kwamitin gudanarwar hukumar IAEA jiya Laraba, da kuma wani kuduri da ake neman amincewa da shi yayin zaman taron da aka shirya kan kasar ta Iran.

Rahotanni na cewa, jami’an diflomasiyya sun bayyana a ranar Talata cewa, kasashen Amurka da Burtaniya da Faransa da Jamus, sun gabatar da wani kuduri ga hukumar IAEA, dake kira ga Iran da ta baiwa hukumar cikakken hadin kai. (Ibrahim Yaya)