logo

HAUSA

Sa’o’i Kalilan Ya Rage Adadin Al’ummar Duniya Ya Kai Biliyan 8

2022-11-15 19:52:20 CMG Hausa

MDD ta tunatarwa al’ummun duniya cewa, an yi hasashen yawan al’ummar duniyar zai kai biliyan 8, a yau Talata, 15 ga wata.

Wata sanarwa da majalisar ta fitar, ta ce wannan ci gaba ne ga bil Adama. Tana mai cewa, karuwar adadin da ba a yi tsammani ba, na da nasaba da karuwar tsawon rayuwar bil Adama saboda ingantuwar tsare-tsaren kiwon lafiya da sinadarai masu gina jiki da kula da tsaftar jiki da muhalli da kuma magunguna.

A cewar sanarwar, yayin da aka dauki shekaru 12 kafin adadin ya kai biliyan 8 daga biliyan 7, za a dauki kimanin shekaru 15, wato sai a shekarar 2037, adadin al’ummar duniya zai kai biliyan 9, alamar dake nuna cewa, saurin karuwar al’ummar duniya na ja da baya.

Sanarwar ta ruwaito sakatare janar na MDD Antonio Guterres na cewa, wannan lokaci ne na murnar kasancewar mabambantan al’ummomi da kuma ci gaban da aka samu, tare kuma da la’akari da hakkin kare duniya dake wuyan daukacin bil Adama. (Fa’iza Mustapha)