logo

HAUSA

Cutar Ebola ta bulla a gabashin kasar Uganda

2022-11-14 10:23:10 CMG Hausa

Ministar ma’aikatar lafiyar kasar Uganda Ruth Aceng, ta ce cutar Ebola ta bulla a yankin gabashin kasar, bayan jimawa da ta yi tana yaduwa a tsakiyar kasar.

Ruth Aceng, wadda ta wallafa hakan a wani sakon Tiwita a jiya Lahadi, ta ce wani mutum mai shekaru 45 da haihuwa, ya rasu a gundumar Jinja dake gabashin Uganda, wanda hakan ke tabbatar da cutar ta kara yaduwa zuwa karin sassan kasar.

Ministar ta ce mutumin ya rasu a gida a ranar 10 ga watan nan, ana kuma hasashen mai yiwuwa ya harbu da cutar ne daga wani dan uwansa da ya yi tafiya zuwa birnin Kampala a kwanakin baya, wanda shi ma ya rasu a ranar 3 ga watan nan, bayan jinyar kwanaki 10 a gundumar Jinja.

Aceng ta ce tuni an fara bibiyar wadanda suka yi cudanya da mamatan, domin dakile ci gaba da bazuwar wannan annoba.

Alkaluman ma’aikatar lafiya a Uganda sun nuna cewa, daga ranar 20 ga watan Satumba, lokacin da aka samu bullar cutar zuwa 6 ga watan nan, an tabbatar da harbuwar mutane 135 da cutar ta Ebola a kasar. (Saminu Alhassan)