logo

HAUSA

Sin na fatan Amurka za ta yi hakuri da bambancin dake tsakaninsu

2022-11-14 20:58:08 CMG Hausa

 

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, ta bayyana fatan Amurka za ta iya hakuri da bambancin dake tsakaninta da Sin domin bangarorin biyu sun cimma matsaya daya.

A cewar kakakin ma’aikatar Mao Ning, manufar kasar Sin dangane da huldarta da Amurka, ba ta sauya ba. Tana mai cewa, Sin na nacewa ga ka’idar mutunta juna da mu’amala cikin lumana da moriyar juna tsakaninta da Amurka. Haka kuma, za ta nace wajen kare ikon mulkinta da tsaro da muradunta na ci gaba.

A cewarta, Sin na fatan Amurka za ta iya hakuri da wasu batutuwa domin tunkarar bambancin dake tsakaninsu ta hanyar da ta dace, da daukaka hadin gwiwa mai ma’ana, da kaucewa rashin fahimta da mayar da dangantakar Sin da Amurka bisa turbar da ta dace.