logo

HAUSA

An jinjinawa matakan Sin na shawo kan kalubalen sauyin yanayi

2022-11-14 10:24:59 CMG Hausa

Mahalarta taron sauyin yanayi na MDD dake gudana yanzu haka, sun jinjinawa matakan da kasar Sin ke aiwatarwa game da shawo kan kalubalen sauyin yanayi.

Da yake tsokaci game da hakan, babban jami’in cibiyar kasa da kasa mai lura da aiwatar da matakan shawo kan sauyin yanayi Patrick Verkooijen, ya ce cikakken shirin shawo kan kalubalen sauyin yanayi na kasar Sin ya ciri tuta. Ya ce Sin ce kadai kasar da ke maida hankali matuka game da yanayin da ake ciki yanzu, da kuma damammakin gobe a fannin sauyin yanayi. 

A nasa bangare kuwa, mashawarci na musamman ga babban sakatare, da mataimakin sakataren MDD mai lura da batun sauyin yanayi Selwin Hart, cewa ya yi aiwatar da matakan shawo kan sauyin yanayi, wanda shi ne babbar matsala ga kasashe masu tasowa, ya jima da zama rabin kaso na kalubale da kasashen ke fuskanta ta fuskar sauyin yanayi.

Jami’in ya ce salon da kasar Sin ke aiwatarwa yana amfanar kasar, yana kuma ba ta damar raba kwarewa da sauran sassan, da fadada hadin gwiwa da sauran kasashe masu tasowa.

Shi ma mataimakin shugaban bankin raya nahiyar Asiya Ahmed Saeed, jinjinawa salon shawo kan sauyin yanayi na Sin ya yi, wanda ya ce kyakkyawan mataki ne dake daga matsayin hadin gwiwar kasa da kasa, mai tasiri wajen shawo kan kalubalen sauyin yanayi. (Saminu Alhassan)