logo

HAUSA

Tawagar kasar Sin ta gudanar da taron gefe kan dabarun yaki da tinkarar sauyin yanayi da Sin ke dauka

2022-11-11 16:38:03 CMG Hausa

Tawagar kasar Sin dake halartar babban taro na 27 game da dabarar tsarin sauyin yanayi ta MDD, ta gudanar da taron gefe kan ayyukan tinkarar sauyin yanayin da Sin ke dauka a ranar jiya Alhamis, agogon wurin. Shugaban tawagar shawarwari kan sauyin yanayi na Sin kuma mataimakin ministan ma’aikatar muhalli ta kasar Mr. Zhao Yingmin ya halarci taron tare da gabatar da jawabi.

Zhao Yingmin ya bayyana a cikin jawabinsa cewa, ragewa da daidaitawa su ne manyan manufofi biyu na tinkarar sauyin yanayi, don haka kamata ya yi a baiwa matakan biyu matsayi daidai, ba kuma tare da yin sakaci ba.

Mai baiwa babban sakataren MDD shawara na musamman kan matakan yaki da sauyin yanayi Selwin Hart, ya taya Sin murnar fitar da dabarunta na tinkarar sauyin yanayi nan da shekarar 2035. Yana mai cewa, wannan dabara tana da matukar muhimmanci ga kasar Sin da ma duniya baki daya, kana wani ci gaba ne, na karfafa hadin gwiwar kasa da kasa don tinkarar matsaloli na sauyin yanayi yadda ya kamata. (Safiyah Ma)