logo

HAUSA

An kashe a kalla mayakan BH 5 a Niger

2022-11-10 13:52:54 CMG HAUSA

 

Ma’aikatar tsaro ta Niger, ta ce sojojin kasar sun kashe a kalla mambobi 5 na kungiyar BH, tare da sakin mutane 7 da suka sace, a yankin Diffa dake iyakar kudancin kasar.

Wata sanarwar da ma’aikatar ta fitar, ta ce bayan mayakan BH sun sace mata 7 da namiji guda a yankin Diffa a ranar Litinin, jami’an tsaron suka fara farautarsu, inda suka kashe a kalla mayaka 5 a ranar Talata, tare da sakin matan da aka sace.

Sai dai, namijin ya rasa ransa sanadiyyar raunika, haka kuma sojoji 3 sun jikkata. (Fa’iza Msutapha)