logo

HAUSA

Wakilin Sin: Nasara da Sin ta cimma na kaiwa kololuwar fitarwa da daidaita iskar Carbon abin a yaba ne

2022-11-07 10:02:47 CMG Hausa

Manzon musamman na kasar Sin kan sauyin yanayi Xie Zhenhua, ya bayyana cewa, kasarsa ta cimma gagarumar nasara wajen cimma burinta na kaiwa ga kololuwa da ma daidata hayakin Carbon. Xie Zhenhua ya bayyana haka ne, a gyefen wani taro mai taken ”Rayuwa ba tare da gurbata muhalli ba, kokarin hadin gwiwa da musayar nasarori- shawarar shigar da jama’a don daukar sabbin matakan kare muhalli” wanda aka yi a rumfar kasar Sin a wajen taro na 27 na bangarorin da suka sanya hannu kan yarjejenyar sauyin yanayi ta MDD (COP27) game da sauyin yanayi. Shi ma shugaban tawagar kasar Sin kana mataimakin minista a ma’aikatar kula da muhalli ta kasar Sin Zhao Yingmin, ya halarci taron.

Xie ya yi nuni da cewa, kasar Sin ta yi nasarar aiwatar da yarjejeniyar sauyin yanayi da aka cimma a birnin Paris na kasar Faransa, ta kuma kara karfafa gudummawar da take bayarwa a fadin kasar, da nufin kaiwa ga kololuwa da ma daidaita iskar Carbon da take fitarwa da cimma nasarar kawar da iskar Carbon cikin ingataccen tsari. Yana mai cewa, kasar Sin ta samu gagarumin ci gaba a wannan fanni.

Alkaluman kididdiga na farko-farko sun nuna cewa, yawan hayakin Carbon dioxide da kasar Sin take fitarwa a kowane kaso na GDPn kasar a shekarar 2021, ya ragu da kaso 3.8 cikin 100 kan na shekarar 2020 da kuma kaso 50.8 cikin 100 kan na shekarar 2005. (Ibrahim Yaya)