logo

HAUSA

Sin: Abubuwan dake cikin rahoton tsaron Amurka na 2022 game da Sin tsohon tunani ne na yakin cacar baka

2022-11-04 19:15:36 CMG Hausa

Game da abubuwan dake da nasaba da kasar Sin dake cikin rahoton tsaron kasa na shekarar 2022 da ma’aikatar tsaron kasar Amurka ta wallafa a kwanakin nan, mai magana da yawun ma’aikatar tsaron kasar Sin Tan Kefei, ya bayyana Jumma’ar nan cewa, wannan wani tsohon tunani ne na yakin cacar baka da kuma rashin kan gado ne.

Don haka, kasar Sin ta bukaci bangaren Amurka, da ya yi fatali da tunanin yakin cacar baka, da kuma kara kaimi don kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya da ma shiyya-shiyya.(Ibrahim)