logo

HAUSA

Yadda Amurka ke kara kudin ruwa ya haifar da damuwa ga masanan tattalin arzikin duniya

2022-11-03 14:28:36 CMG Hausa

Yau Alhamis, babban bankin Amurka ya sanar da kara kudin ruwa da kaso 0.75 bisa dari, kuma, wannan shi ne karo na hudu da babban bankin na Amurka ya sanar da kara kudin ruwan da kaso 0.75 bisa dari, kana, karo na shida da babban bankin kasar ya sanar da kara ruwan kudi a bana, lamarin da ya janyo damuwa tsakanin al’ummomin kasa da kasa.

Dangane da wannan batu, shirin talabiji mai taken “tattalin arzikin duniya”, na babban gidan rediyo da talabijin na kasar Sin(CMG), da kwalejin gudanar da harkokin kasa da nazarin ra’ayin jama’a na jami’ar Renmin ta kasar Sin, sun gayyaci masanan tattalin arzikin duniya guda 100, domin su bayyana ra’ayoyinsu kan batun. Masanan dai na ganin cewa, yadda kasar Amurka ke ci gaba da kara kudin ruwa, zai gaggauta raguwar tattalin arzikin duniya, kuma, kaso 90 daga cikinsu, suna ganin cewa, ana fuskantar karin kalubalen hauhawar farashin kaya sakamakon wannan mataki, kana, kaso 94 daga cikinsu, na ganin cewa, ci gaba da kara kudin ruwan za haddasa karin barazanar basussuka ga kasashe maso tasowa.

Yadda babban bankin kasar Amurka ke ci gaba da kara kudin ruwa, ya haddasa damuwar kasuwannin duniya kan tattalin arziki. Bisa bayanin da aka fitar, kaso 73 bisa dari na masanan da aka zanta da su, suna ganin cewa, matakin zai haddasa illa ga yanayin tattalin arzikin duniya, kuma kaso 88 bisa dari daga cikinsu, suna ganin cewa, hakan zai kawo barazana ga kasuwannin sha’anin kudi na kasashen duniya. Bugu da kari, kaso 82 bisa dari na masanan na ganin cewa, matakin ya bata ran ‘yan kasuwa da masu zuba jari. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)