logo

HAUSA

Jakadan Sin dake Nijeriya ya kai ziyarar aiki jihar Edo

2022-11-03 11:12:27 CMG Hausa

Jakadan kasar Sin dake Nijeriya Cui Jianchun, ya kai ziyarar aiki jihar Edo dake kudancin kasar, inda ya gana da gwamnan jihar Godwin Obaseki, tare da ziyartar kamfanonin kasar Sin dake jihar.

A yayin ganawa da gwamna Obaseki a ranar Talata, jakada Cui Jianchun ya yi fatan karfafuwar hadin gwiwa tsakanin jihohi da yankunan Sin da Nijeriya, ya kuma yi fatan sa kaimi ga karin kamfanonin kasar Sin, domin su zuba jari, da kafa rassan kamfanoninsu a Nijeriya, domin inganta bunkasuwar harkokin masana’antu a kasar, bisa manufar raya hadin gwiwa tsakanin Sin da Nijeriya karkashin manufar nan mai lakabin 5GIST, da kuma yin mu’amala kan al’adun kasar Sin, karkashin manufar yin hadin gwiwa da nuna fahimtar juna, ta yadda kasashen biyu za su ci gaba da karfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu.

A nasa bangare kuwa, Godwin Obaseki ya ce, kamfanonin kasar Sin sun samar da guraben ayyukan yi da dama ga al’ummun jihar Edo, da samar da haraji ga gwamnatin jihar, da kuma ba da taimako ga jihar a fannin horar da masana fasaha, lamarin da ya ba da gudummawa ga raya harkokin masana’antun kasar. Daga nan sai ya yi fatan za a karfafa mu’amala tsakanin jami’an kasashen biyu, da kuma sa kaimi ga karin kamfanonin kasar Sin don su zuba jari a jihar Edo. Ya ce tabbas, jihar za ta samar da yanayin kasuwanci mai kyau ga kamfanonin kasar Sin, ta yadda za su gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.

A halin yanzu, akwai kamfanonin kasar Sin sama da 20 dake jihar Edo, wadanda suke gudanar da ayyukan sarrafa karfe, da gilashi, da kayayyakin fadi-ka-mutu, da kayayyakin katako da dai sauransu, sun kuma samar da guraben aikin yi kimanin dubu 6 ga mazaunan wurin. (Maryam)