logo

HAUSA

An fara rangadin nuna kashi na uku na fina-finan kasar Sin a Afirka

2022-11-03 19:09:35 CMG Hausa

Tun daga watan Nuwamba ne, kafofin watsa labaran Afirka guda 14 suka fara nuna wasu kayatattun fina-finan kasar Sin guda 17 da aka fassara cikin harsunan Turanci da Faransanci da Swahili da Hausa da harshen Larabci. Inda masu kallo daga kasashen na Afirka za su kalli fina-finan cikin harsunansu na gida a cikin kasashensu.

Babban rukunin gidan rediyo da talabijin na kasar Sin ne wato CMG, ya aika kunsin kyautar wadannan fina-finai, inda za a watsa su a kafafen watsa labarai 14 na kasashen Afirka da suka hada da gidan talabijin na kasar Uganda da hukumar watsa labarai ta kasar Kenya da gidan rediyo da talabijin na Burundi da gidan talabijin na kasar Madagascar.

Wadannan fina-finai, za su baiwa masu kallo na kasashen Afirka damar kara fahimtar tunanin al’ummar Sinawa da zaman jituwa tsakanin bil-Adama da muhalli, da fadi tashi na aiki tukuru da kyakkyawar abokantaka dake tsakanin al’ummomin Sinawa da na Afirka. (Ibrahim)