logo

HAUSA

Sin na fatan gamayyar kasa da kasa za su dukufa wajen kare ’yan gudun hijira

2022-11-03 11:08:11 CMG Hausa

A jiya Laraba ne mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Geng Shuang, ya gabatar da jawabi, bayan ya saurari rahoton babban kwamishinan kula da harkokin ’yan gudun hijira na MDD, yayin zaman kwamitin sulhu na majalissar. Geng Shuang ya ce, kasar Sin za ta ci gaba da nuna goyon baya ga ayyukan hukumar kula da ’yan gudun hijira ta MDD, da manyan jami’ai masu kula da ’yan gudun hijira, kuma, tana fatan gamayyar kasa da kasa za su gaggauta aikin tattara kudade, domin kiyaye dukkanin ’yan gudun hijira yadda ya kamata.

Jami’in na Sin ya kara da cewa, a bana, yawan ’yan gudun hijira, da wadanda suka kasa komawa gidajensu ya zarce miliyan 100, wanda hakan ya sa ake bukatar karin taimakon jin kai gare su, kuma kawo yanzu ba a samu isasshen taimakon jin kai gare su ba. Ya ce a halin yanzu, kasashe masu tasowa ne suka karbi kaso 83 bisa dari na jimillar ’yan gudun hijirar duniya, don haka ya kamata kasashe masu ci gaba su sauke nauyin dake wuyan su, kuma su cika alkawuran da suka yi na taimakawa kasashe masu tasowa a wannan fanni.

Ya kuma kara da cewa, nahiyar Afirka ita ce ta fi fama da matsalar ’yan gudun hijira, kuma kasar Sin tana fatan hukumar ’yan gudun hijira ta MDD, za ta ci gaba da sanya wadannan ayyuka kan gaba a nahiyar Afirka, domin samar wa kasashen nahiyar taimakon kudi, da goyon baya, ta yadda za a samarwa ’yan gudun hijirar nahiyar taimakon da suke bukata.   (Mai Fassarawa: Maryam Yang)