logo

HAUSA

Najeriya na aiwatar da matakan kandagarki sakamakon bullar Ebola a Uganda

2022-11-01 13:57:09 CMG Hausa

 

Hukumomin lafiya a tarayyar Najeriya, na aiwatar da matakan kandagarki a kan iyakokin kasar, bayan da aka tabbatar da bullar cutar Ebola a kasar Uganda.

Wata sanarwa da cibiyar kandagarki da yaki da cututtuka ta kasar ko NCDC ta fitar, ta ce an kara kaimi wajen tantance lafiyar fasinjoji dake dawowa kasar daga Uganda a filayen jirgin saman Najeriya, kana mahukuntan kasar na jan kunnen al’umma da su kaucewa yin tafiye-tafiye da ba su zama dole ba zuwa Uganda.

A cewar shugaban cibiyar ta NCDC Ifedayo Adetifa, ana jan hankalin ’yan kasar ne a wani mataki na tabbatar da cutar ta Ebola ba ta samu damar shiga Najeriya ba.

Adetifa ya kara da cewa, mahukuntan lafiya na kira ga ’yan Najeriya da suka dawo daga Uganda a baya bayan nan, ko wadanda sun bi ta kasar yayin balaguro cikin makwanni 3 da suka gabata, da su lura da alamun cutar da ka iya bayyana a jikin su, don tabbatar da dakile bazuwar ta.   (Saminu Alhassan)