logo

HAUSA

Xi Ya Jagoranci Shugabannin JKS Zuwa Tsohuwar Hedkwatar Jam’iyyar

2022-10-27 20:08:47 CMG Hausa

Sakatare janar na kwamitin tsakiya na Jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin Xi Jinping, ya jagoranci mambobin zaunannen kwamitin ofishin kula da harkokin siyasa na kwamitin tsakiyar jam’iyyar, domin ziyartar Yan’an, wato tsohuwar hedkwatar JKS, wadda ke lardin Shaanxi na arewa maso yammacin kasar.

Xi Jinping, wanda kuma shi ne shugaban kasar, kuma shugaban rundunar sojinta, ya samu rakiyar wasu daga cikin shugabannin jam’iyyar da suka hada da Li Qiang da Zhao Leji da Wang Huning da Cai Qi da Ding Xuexiang da kuma Li Xi.

Sun kuma ziyarci wajen da babban taron wakilan JKS karo na 7 ya gudana, da gidan tsohon shugaban kasar Mao Zedong, da kuma dakin nune-nunen tunawa da juyin juya halin jam’iyyar na Yan’an, wanda ke dauke da tarihin lokacin da hedkwatar kwamitin tsakiyar JKS ke zaune a Yan’an, tsawon shekaru 13. (Fa’iza Mustapha)