logo

HAUSA

Hadaddiyar Daular Larabawa ta fara aiwatar da manufar kin baiwa ‘yan Najeriya Biza

2022-10-27 11:12:47 CMG Hausa

Jaridar “This Day” da ake wallafawa a Najeriya, ta wallafa wani labari dake cewa, kwanan baya hukumar masarautar Hadaddiyar Daular Larabawa ta sanar da cewa, za ta aiwatar da manufar hana daukacin ‘yan Najeriya Bizar shiga kasar, ba tare da mayar musu da kudin da suka biya ba.

Duk da cewa hukumar ba ta bayyana ainihin dalilin yin hakan ba, amma ta ce an dakatar da baiwa ‘yan Najeriyar Biza, har zuwa lokacin da za a daidaita matsalar da ta kunno kai tsakanin gwamnatocin kasashen biyu. (Jamila)