logo

HAUSA

Shugabannin JKS na shirye-shiryen aiwatar da ruhun babban taron JKS karo na 20

2022-10-25 19:56:14 CMG Hausa

 

Ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na JKS ya kira taro a yau Talata, domin shirya yadda za a yi nazari da yayata tare da aiwatar da ruhun babban taron wakilan JKS karo na 20.

Sakatare Janar na kwamitin tsakiyar, Xi Jinping, shi ne ya jagoranci taron, wanda ya kuma tattauna kan ka’idojin karfafawa da kare cikakken iko da hadin kan shugabancin jam’iyyar da kuma ka’idojin aiwatar da matakai 8 da aka dauka kan yanayin gudanar da aiki. (Fa’iza Mustapha)