logo

HAUSA

Sunak na shirin zama firaministan Burtaniya

2022-10-25 10:01:51 CMG Hausa

Tsohon sakataren kudin Burtaniya, Rishi Sunak ya lashe zaben shugabancin jam’iyyar Conservative mai mulki jiya Litinin. Zai kuma maye gurbin Liz Truss a matsayin sabon firaministan kasar.

Sunak shi ne mutum daya tilo da ya samu goyon bayan ‘yan majalisu 100 da ake bukata, ya zuwa karshen wa’adin da aka tsayar wato karfe 2 na rana agogon kasar, abin da ya ba shi damar samun nasara kai tsaye.

Takarar shugabancin dai ta bijiro ne, lokacin da Truss ta sanar da yin murabus a ranar Alhamis, bayan shafe kimanin sama da makonni 6 a kan wannan mukami. (Ibrahim)